Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hatimin Amurka



Hatimin Amurka Hoto: The White House


Hatimin Gwamnatin Amurka, shi ne a hukumance ke nuna ingancin dukkanin wata takarda ko kundin yarjejiya, fasfo da sauransu na Ƙasar Amurka.

Government Info (2020), sun bayyana shi da cewa: “Babban hatimi yana alamta ‘yancin gwamnatin gashin-kai; wadda yake bayyana a dukkan wasu takardu da suka haɗa da sanarwowi, yarjeniyoyi, da takardun sadarwa daga shugaban ƙasa da kuma shugabannin gwamnatocin waje. Shi ne kuma yake bayyana a fasfon ƙasar Amurka da kuma jikin takardar kuɗin Amurka dala ɗaya.”


Fasfon Amurka ɗauke da hatimi
Hoto:US Department of State


Fasfon Amurka ɗauke da hatimi
Hoto:US Department of State

Da zarar samun ‘yancin kan Ƙasar Amurka a cikin shekarar 1776 aka ƙaddamar da wani kwamatin musamman da ya yi shekaru 6 cur yana tayin samfura daban-daban na hatimin da zai kasance wa ƙasar Amurka hatimi a hukumance amma duka basu dace ba.

Daga ƙarshe, a cikin shekarar 1782 aka ɗora alhakin samar da hatimin ga sakataren kwamatin mai suna Charles Thomson wanda shi kuma ya wassafa shi a rubuce inda rubutun ya samu amincewar kwamatin tare kuma da damƙa alhakin mayar da shi hoto inda aka sake haɗa shi da wani baturen mai suna William Barton. Waɗannan mutane guda biyu su ne suka haɗu suka tsara wannan hatimi a zahirance gabansa da bayansa.

Manazarta:

Government Info (2020). The Great Seal of the United States. An Ciro a 2021, daga https://www.govinfo.gov/features/great-seal



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub